'Yan adawar Kamaru sun hade – DW – 10/06/2018
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan adawar Kamaru sun hade

October 6, 2018

Sa'o'i gabanin fara kada kuri'a a zaben kasar Kamaru 'yan adawa a sun hade waje guda don ganin sun kwace mulki daga hannun Shugaba Paul Biya.

https://p.dw.com/p/3657u
Kamerun Präsidentschaftswahlen l Maurice Kamto MRC
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Wasu jam'iyyun adawa a Kamaru sun sanar da shirin dunkulewa waje guda, don ganin sun kwace mulki daga hannun Shugaba Paul Biya mai ci a babban zaben kasar da za a yi a ranar Lahadi.

Jagoran jam'iyyar FDP Akere Muna, ya janye daga takarar shugabanci da yake yi, don kara wa dan takara a jam'iyyar MRC Maurice Kamto karfin iya tinkarar Shugaba Biya mai shekaru 85.

Sai dai hadakar ba ta hada da dan takaran jam'iyyar SDF ba, wato Joshua Osih.

Ko a jiya Juma'a ma Maurice Kamto na jam'iyyar MRC, ya yi zargin ana tsara wani gagarumin magudi don bai wa Shugaba Biya damar zarcewa kan mulki karo na bakwai a Kamarun.

Jam'iyyar ta ce ana can ana ci gaba da rajistar masu zabe da aktunan boge a wasu wuraren, duk da cewar wa'adin rajistar ya shude.