Shugaban Ukraine ya sake mika kokon bara a Amurka – DW – 12/12/2023
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Ukraine ya sake mika kokon bara a Amurka

December 12, 2023

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya isa kasar Amurka a wani salo na babu yabo kuma ba fallasa, sabanin a shekarar da ta gabata da ya sha tarba daga hukumomin kasar.

https://p.dw.com/p/4a4be
Hoto: Sean Gallup/Getty Images

 

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy, ya isa kasar Amurka a wani salo na babu yabo kuma ba fallasa, sabanin a shekarar da ta gabata da ya sha tarba daga hukumomin kasar.

Ziyarar ta sa na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban Amurka Joe Biden ya mika bukatar karin dala bilyan 110 ga kasashen Ukraine da Isra'ila da sauran batutuwan da suka shafi tsaro a zauren majalisar dokokin kasar da wannan kuduri ke shan suka daga wasu daga cikin 'yan majalisar.

Fadar White House ta ce ziyarar ta zo akan gaba da shugaban Amurka ke fadi tashin ganin an samarwa Ukraine karin tallafin yakin da ta ke yi da kasar Rasha, to amma 'yan majalisar sun yai fatali da wannan bukata. Guda daga cikin na hannun damar Joe Biden, Sanata Chris Coons, ya ce wannan abin kunya ne ga Ukraine dama al'ummar kasar baki daya.

Gabanin ziyarar ta Zelensky zuwa Amurka, wasu bayanan sirri sun tabbatar da cewa Ukraine ta sha kashi a hannu Rasha kama daga asarar tankunan yaki sama da 220 da kuma sojoji da yakin ya rutsa 13,000 a gwabzawar baya-bayannan a mashigin Avdiivka-Novopavlivka.