Sabon nau'in Polio ya bulla a wasu sassan Najeriya – DW – 09/24/2024
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon nau'in Polio ya bulla a wasu sassan Najeriya

Uwais Abubakar Idris MAB
September 24, 2024

Hukumomin lafiya sun bayyana cewar an samu nau'i na biyu na shan Inna da ya kama yara 70 a kanana hukumomi 46 da ke jihohi 14 na arewacin Najeriya, abin da ya sanya nuna damuwa saboda cutar na illata lafiyar yara kanana.

https://p.dw.com/p/4l27n
Hukumomin Najeriya sun juma da fara yaki da cutar Polio da ke addabar yara kanana
Hukumomin Najeriya sun juma da fara yaki da cutar Polio da ke addabar yara kananaHoto: picture-alliance/dpa/M. Wolfe

Kasa da makonni biyu bayan da Najeriya ta sanar da sake bullar cutar shan Inna a kasar ne hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewar kananan hukumomi 46 na jihohi 14 ne aka samu nau'i 14 na biyu na cutar, abin da ya nuna cewar aiki na neman komawa baya ga Najeriya. Idan za a iya tunawa, kasar ta yi gagarumin biki a 2020 na sallamar cutar Polio, amma bakon da aka yi sallama da shi bai yi  nisa ba yanan nan labe.

Karin bayani: Najeriya: Shirin bankwana da Polio

Shugaban hukumar lafiya matakin farko ta Najeriyar Dr Muyiwa Aina ya ce wannan na nuna ci-gaba da yaduwar cutar Polio da ake samu, wanda dole ne a dauki mataki. Akwai matsaloli mabambanta da ake dangata su da dalilin sake bullar cutar Polio da ma yaduwarta a wadannan jihohi 14 da hukumar bata bayyana su ba saboda wasu dalilai.

Wadanda cutar Polio ta nakasa sun hada kansu a Jos don koyan sana'o'i
Wadanda cutar Polio ta nakasa sun hada kansu a Jos don koyan sana'o'iHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

A mafi yawancin jihohin arewacin Najeriyar, an fuskanci matsaloli na tashe-tahsne hankula musamman na ayyukan ta’adanci da masu ‘yan bindigar daji da suka katse hanzari na masu rigakafi a yankuna da dama. Babban aiki ne ke gaban hukumomii na ci gaba da wayar da kan jama’a a kan wannnan lamari. 

Karin bayani: An kawar da Polio daga nahiyar Afirka

Hukumar lafiya a matakin farko ta sake farafdo da tarurruka da sarakunan gargajiya da shugabanin addinai a Najeriya, a kokarin sake shawo kan wannan matsalarPolio  da ta sake kuno kai, inda a wannan karon ta gudanar da taro a karkashin inuwar cibiyar wanzar da zaman lafiya ta mai alkfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda ya bukaci hadin kai don yakar cutar. Ita ma hukumar lafiya a matakin farko ta bayyana cewa Najeriya na asarar yara kanana da ba su kai shekaru biyar da haihuwa ba har 2,300, abin da ke nuna rashin karuwar hanyoyin kula da lafiya musamman a yankunan karkara.