Shugaban Kamaru ya yi afuwa ga fursunonin siyasa – DW – 10/03/2019
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Kamaru ya yi afuwa ga fursunonin siyasa

Abdourahamane Hassane
October 3, 2019

Fursunonin siyasa 333 gwamnatin Kamaru ta ba da sanarwa yi musu afuwa a wani mataki na samun bakin zaren rikicin 'yan aware na kasar.

https://p.dw.com/p/3QhLj
Kamerun Präsident Paul Biya
Hoto: picture-alliance/Photoshot/Ju Peng

Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya ya yi wa 'yan aware da aka ake zargi da hannu cikin rikicin sashin Inglishi 333 afuwa wadanda ake tsare da su a gidajen fursuna dabam-dabam na Kamaru. Wannan afuwa na zuwa ne a kwanaki hudu na tattaunawa ta kasa baki daya da ake ci gaba da yi da nufin warware rikicin 'yan awaren da kawo yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban rayukan jama'a.