Merkel ta goyi bayan tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya – DW – 05/18/2021
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Merkel ta goyi bayan tsagaita wuta a Gabas ta Tsakiya

May 18, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta tattauna ta bidiyo da Sarki Abdullah na Jordan kan tashin hankalin da ake gani a Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/3tZil
3. Ökumenische Kirchentag 2021
Hoto: oekt.de

Tattaunawarsu ta wannan Talata ta nuna bukatar samun tsagaita wuta, a cewar mai magana da yawun shugabar gwamnatin Jamus.

Wannan na zuwa ne a yayin da a dazu da rana, ma'aikatar lafiyar Falasdinu ta ce wani mutum guda daya ya rasa ransa, wasu kuma sun ji munanan raunuka a artabun da aka yi a tsakanin matasan Falasdinawan da sojojin Izra'ila.

Matasan a sassa daban-daban na Izra'ila da yammacin kogin Jodan sun rinka kona tayoyi tare da yi wa sojojin Baniyahudun ruwan duwatsu, a yayin da su kuma sojojin suka mayar da martani da harba hayakin da ke sanya kwalla.