Isra'ila ta gargadi mayakan Hezbollah – DW – 09/23/2024
  1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta gargadi mayakan Hezbollah

Suleiman Babayo ATB
September 23, 2024

Sojojin Isra'ila sun fitar da sanarwar cewa sun kai farmaki kan daruruwan wurare cikin kasar Lebanon domin kara saka matsin lamba kan tsagerun kungiyar Hezbollah da ke gwagwarmaya da makamai.

https://p.dw.com/p/4kzji
Motoci a Lebanon da ke ficewa daga wuraren da ake kai hare-haren Isra'ila
Motoci a Lebanon da ke ficewa daga wuraren da ake kai hare-haren Isra'ilaHoto: Amr Abdallah Dalsh/REUTERS

Wata majiya ta kusa da mayakan Hezbollah na Lebanon ta ce hare-haren da dakarun Isra'ila suka a kudancin birnin Beirut fadar gwamnatin kasar sun ritsa da daya daga cikin wuraren da kungiyar take gudanar da ayyukanta. Daruruwan farmaki dakarun Isra'ila suka kaddamar a yankunan kudanci da gabashin Lebanon a wannan Litinin.

Fiye da mutane 270 suka halaka sakamakon hare-haren na dakadun Isra'ila yayin da wasu darauruwa suka jikata.

Tuni Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila ya yi gargadi kan abin da 'yan Hezbollah za su fuskanta daga dakarun kasarsa. Firaministan ya bayyana cewa mayakan Hezbollah za su fuskanci sakamakon jefa rayuwar 'yan Isra'ila cikin kasada da suka yi.